Home Labaru Babu Wanda Ya Kara Farashin Mai A Nijeriya – NNPCL

Babu Wanda Ya Kara Farashin Mai A Nijeriya – NNPCL

23
0

Shugaban kamfanin mai na NNPC Mele Kyari, ya ce babuwanda ya kara farashin man fetur a Nijeriya.

Mele Kyari, ya musanta iƙirarin da wasu kungiyoyin masudakon mai su ka yi a baya cewa an ƙara farashin man fetur.

Shugaban kamfanin NNPC ya bayyana haka ne, yayin wanitaron masu ruwa da tsaki da ya gudana a kan matsalarkarancin man fetur da ake fama da ita.

Mele Kyrai, ya kalubalanci duk masu ruwa da tsakin da su kahalarci taron, su bayyana wanda ya ce kara farashin man feturko kuma su gabatar da hujjar sun saye shi a sabon farashin dasu ka yi ikirari.