Home Labaru Dattawan Igbo Sun Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Saki Nnamdi Kanu

Dattawan Igbo Sun Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Saki Nnamdi Kanu

11
0

Ƙungiyar dattawan ƙabilar Igbo, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta bada damar zaman tattaunawar sulhu domin a saki shugaban ‘yan A-Waren Biafra Nnamdi Kanu.

Haka kuma, Ƙungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta janye sojojin da ta tura yankin Kudu-Maso Gabashin Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce zaman sojoji a yankin kudancin Nijeriya zai iya kasancewa wata barazana ga lamarin tsaro ga zaɓen gwamnan jihar Anambra.

Ida dai ba a manta ba, shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Mahmud Yakubu, ya bada tabbacin gudanar zaben jihar Anambra cikin kwanciyar hankali, wanda zai gudana ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba na shekara ta 2021.