Home Labaru Kasuwanci Daminar Bana: An Yaba Da Yadda Amfanin Gona Ke Yin Kyau

Daminar Bana: An Yaba Da Yadda Amfanin Gona Ke Yin Kyau

147
0
Good Agricultural Production

A kokarin da manoma keyi na wadata Najeriya da Abinci, an yaba da gudumawar da kamfanoni  magungunan feshi ke bayarwa na samar da magani da Suke taimakawa gona fitar da tsabar Abinci Mai tarin yawa da kuma kyau

Shugaban kamfanin Saida Maganin feshi na Elkhadija Agro Najeriya Limited Shehu Lawal Ramin Kura ya bayyana haka lokacin da yake Karin Haske dangane da yadda amfanin Gona ya yi yabanya a daminar bana

Shehu Ramin Kura, yace duba da fitar amfanin da aka shuka a Wannan shekarar abin godiya ga Allah ne da Kuma yabawa magungunan feshi da manoma suka yi aiki da shi yayin fara shuka dama bayan fitar amfanin, dan haka ya bukaci manoma su kara himma wajen bin ka’idoji da dokokin da aka gindaya gabannin fara aikin feshi domin gudun tafka asara musamman a wannan lokaci da Ake tsakiyar aikin gona.

Shuhu Ramin Kura ya Kara da cewa la’akari da yadda Wasu manoma suke yin sakaci har maganin feshi ya kona musu gona, hakan nada Nasaba ne da kaucewa ka’ida kafin fara aikin.

  

Alhaji Shehu Lawal mai kayan Feshi Ramin kura, ya yi  kira ga Gwamnati ta Kara Rubanya tallafin dake ba bagaran noma domin Kara Samar da aiyukan yi ga matasa wanda a Yanzu Suke sahun gaba a harkar noma.

Leave a Reply