Home Labaru Samar Da Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Bayar Da Umarnin Rufe Wasu Kasuwanni...

Samar Da Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Bayar Da Umarnin Rufe Wasu Kasuwanni A Jihar

51
0

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayar da umarnin rufe dukkan kasuwannin da ke ci mako-mako a jihar tare da taƙaita safarar kayan abinci.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar a yammacin Juma’a ta ce daga yanzu an hana sayar da man fetur a gefen titi wato ‘yan bumburutu, sannan kuma an haramta zuba shi a cikin jarka.

Kazalika, an haramta wa gidajen mai da ke ƙauyuka sayar da man sai a birnin Gusau da kuma hedikwatar ƙananan hukumomin jihar kaɗai.

Haka nan, gwamnan ya bayar da umarnin dakatar da shiga da kuma fitar da kayan abinci daga Zamfara, Sai dai za a ci gaba da harkokin a cikin jihar amma da sharaɗin sai mai shi ya yi cikakken bayanin inda zai kai kayan.

Mai taimaka wa gwamnan Zamfara kan kafofin yaɗa labarai, Zailani Bappa, ya ce an ɗauki matakan ne da zummar daƙile yi wa ‘yan fashin daji safarar kayayyakin zuwa cikin dazukan jihar.

Jerin matakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan ‘yan fashin dajin sun sako ɗaliban Kwalejin Aikin Noma da Kiwon Dabbobi da suka sace a Bakura.