Home Labaru Damfara: Amurka Ta Bada Umurnin A Kamo Shugaban Air Peace Allen Onyema

Damfara: Amurka Ta Bada Umurnin A Kamo Shugaban Air Peace Allen Onyema

279
0
Allen Onyeama, Shugaba Kuma Mamallakin Kamfanin Jiragen Sama Na Air Peace
Allen Onyeama, Shugaba Kuma Mamallakin Kamfanin Jiragen Sama Na Air Peace

Wata kotu da ke yankin Georgia a kasar Amurka, ta bada umarnin kama shugaba kuma mamallakin kamfanin jiragen sama na Air Peace Allen Onyeama.

Kamar yadda takardar da ke dauke da umarnin kama hamshakin attajirin da alkalin kotun mai shari’a Anand ya sanya wa hannu, ta bada umarnin ofishin babban sojin Nijeriya ya adana shi.

Wannan yarjejeniya da ke tsakanin Nijeriya da kasar Amurka, wadda ta amince da kama dan kasar Amurka ko Nijeriya da ake zargi da wani ta’addanci ce za ta fara amfani.

Idan dai ba a manta ba, rahotanni sun ce ofishin ministan shari’a na kasar Amurka ya fitar da takardar da ke bayyana zargin shugaban kamfanin Air Peace da laifin damfara .

Ana zargin sa ne da damfarar banki da almundahanar kudi, inda ya tura kudi kimanin dala miliyan ashirin daga Nijeriya zuwa wani asusun banki na kasar Amurka, ta wata cibiya da ke da takardun bogi a kan sayen wasu jiragen sama.

Sai dai Onyema ya musanta wannan zargi, tare da cewa ba ya da laifi, saboda duk kudaden da aka tura sai sun ratsa ta babban bankin Nijeriya, kuma bai taba yin wani kasuwancin da ba halastacce ba.