Home Labaru Iyalan Maina Sun Bukaci A Sauya Alkalin Da Ke Gudanar Da Shari’ar...

Iyalan Maina Sun Bukaci A Sauya Alkalin Da Ke Gudanar Da Shari’ar Faisal

237
0
Iyalan Maina Sun Bukaci A Sauya Alkalin Da Ke Gudanar Da Shari’ar Faisal
Iyalan Maina Sun Bukaci A Sauya Alkalin Da Ke Gudanar Da Shari’ar Faisal

Iyalin Abdulrasheed Maina, sun bukaci shugaban babbar kotun tarayya mai shari’a John Tsoho ya sauya alkalin da ke shari’a tsakanin gwamnatin tarayya da Faisal Abdulrasheed Maina.

Sun ce ba su da kwarin gwiwa a kan mai shari’a Okon Abong na babbar kotun tarayya ta 6 da ke Abuja.

Iyalin Maina dai sun bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawun su Usman Abdullahi, cewa sun shigar da bukatar sauya alkalin domin tsoron yiwuwar rashin adalci da Faisal Maina zai iya fuskanta.

Biyo bayan bukatar da iyalan Maina su ka tura ta hannun lauyan su, akwai kuma bukatar mai shari’a John Tsoho ya maida shari’ar zuwa hannun wani alkali banda Okon Abang, domin akwai yiwuwar Faisal ba zai samu adalci ba,

Yayin da ya ke maida martani, alkalin ya yi kokarin musanta abin da ake zargin sa a kan Maina, inda ya ce kawai wannan kokari ne na ganin yadda za a maida shari’ar hannun alkalin da za su iya juyawa yadda su ke so.