Home Labaru Dambarwar Kwaya: An Bada Belin Wanda Ya Sanya Kwaya A Kayan Zainab...

Dambarwar Kwaya: An Bada Belin Wanda Ya Sanya Kwaya A Kayan Zainab Aliyu

737
0

Mai taimaka wa shugaban kasa a kan harkokin kasashen waje Abike Dabiri-Erewa, ta ce an bada belin mutumin da ake zargi da sa kwayar Tramol a jakar Zainab Aliyu da hukumomin kasar Saudiyya su ka kama bisa zargin ta da safarar kwayoyi.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Talatar da ta gabata ne, hukumomin Saudiyya su ka saki Zainab bayan ta shafe kusan kwanaki 6 a gidan yarin kasar.

Bbabban sakatare a ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Nijeriya, ya ce yanzu haka Zainab Aliyu ta na ofishin jakadancin Nijeriya da ke kasar Saudiyya.

Haka kuma, ya ce hukumomin kasar Saudiyya za su saki wani dan Nijeriya Ibrahim Abubakar, wan da ya samu irin matsalar Zainab a kasar Saudiyya.

Sai dai, Dabiri-Erewa ba ta bada cikakken bayani a kan mutumin da aka bada belin ba, sannan ba ta bayyana a wace kotu aka gurfanar da shi ba.