Babban Daraktan hukumar Tsaro ta farin kaya DSS Yusuf Bichi, ya danganta wasu daga cikin matsalolin tsaron da ake fuskanta a Nijeriya da yadda shugabannin siyasa su ka fi gaskata bokaye da matsubbata fiye da jami’an tsaro.
Ya ce ‘yan siyasa da dama sun mika rayuwar su kacokam ga bokaye da matsafa domin magance masu matsalar tsaro.
Bichi ya bayyana haka ne, a wajen wani Taron Sanin Makamar Aiki da aka Shirya wa Zababbun Gwamnoni da wadanda su ka samu nasarar zarcewa.
Daraktan ya kuma yi korafin cewa, akwai babbar matsalar rashin samun bayanan sirri daga karkara, saboda akwai gibi tsakanin shugabannin siyasa da kuma shugabannin gargajiya.