Home Labaru Dambarwa: Sarkin Kano Ya Musanta Zargin Almubazzarantar Da Naira Biliyan 3.4

Dambarwa: Sarkin Kano Ya Musanta Zargin Almubazzarantar Da Naira Biliyan 3.4

773
0

Fadar mai martaba sarkin Kano, ta musanta zargin da hukumar yaki da rashawa da sauraren koke-koken jama’a ta jihar Kano ke yi mata, tare da mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II na almubazzarantar da naira biliyan 3 da milyan 4.

Walin Kano Alhaji Mahe Bashir, ya ce zarge-zargen da ake yi wa masarautar ba su da tushe balle makama, kuma ya bayyana yadda masarautar ta kashe kudaden ta.

Ya ce sabon Sarki bai gaji naira biliyan hudu daga asusun masarautar Kano ba, abin da Sarki Muhammadu Sunusi ya gada shi ne naira biliyan daya da dubu dari takwas da casa’in da uku da dubu dari uku da saba’in da takwas da naira dari tara da ashirin da bakwai da kobo talatin da takwas.

Walin Kano, ya ce masarautar ta biya ‘ya’yan marigayi Sarki Ado sama da naira miliyan dari a matsayin kudin fansar wasu motocin alfarma da fadar ke amfani da su, saboda a cewar su ba motocin masarauta ba ne kyauta aka ba mahaifin su.

Haka kuma, sakamakon harin da aka kai wa tsohon Sarki, masarautar ta sayo motocin sulke guda biyu akan naira miliyan 142 da dubu 800 tare da amincewar gwamnatin jihar Kano.

Leave a Reply