Home Labaru Kiwon Lafiya Kiwon Lafiya: Mazauna Yankin Abuja Sun Koma Ga Masu Maganin Gargajiya

Kiwon Lafiya: Mazauna Yankin Abuja Sun Koma Ga Masu Maganin Gargajiya

1004
0

Mazauna wasu garuruwan da ke karkashin kulawar birnin tarayya Abuja, sun ce sun gwammace su garzaya wajen Bokaye domin neman maganin cututtukan da ke kama ‘ya’yan su maimakon zuwa asibiti saboda ya yi masu nisa.

Wata likitar gargajiyya mai suna Fatima Yusuf, ta ce ta dade ta na duba yara, kuma ta na ba iyaye magani domin warkar da ‘ya’yan su idan su ka kamu da ciwo.

Fatima, ta ce ta na samo magungunan ta ne a cikin kungurmin daji, kuma a duk lokacin da ta ba yaro sai a ga ya samu sauki ya warke.

Wani dattijo mai suna Musa Sarki ya bayyana cewa, ya gaji sana’ar ne daga iyaye da kakanni, kuma ya shi ne kawai zai iya hada surkullen da zai yi wa marar lafiya aiki, sannan su kan shiga cikin kungurmin daji ne don nemo ganyayyakin da su ke amfani da su wajen hada magunguna.

Leave a Reply