Home Labaru Zaben Zamfara: Hukuncin Kotun Koli A Zamfara Jarrabawa Ce Daga Allah –...

Zaben Zamfara: Hukuncin Kotun Koli A Zamfara Jarrabawa Ce Daga Allah – Wamakko

562
0

Shugaban kungiyar sanatocin arewa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayyana hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zaben jihar Zamfara a matsayin jarrabawa daga Allah.

Kotun dai ta soke dukkan kuri’un da aka jefa wa jam’iyyar APC, yayin da ta kaddamar da ‘yan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wadanda su ka lashe zaben.

Sanata Wamakko ya bayyana hakan ne, a lokacin da ya jagoranci wata ziyarar ban-girma da su ka kai wa tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari Abubakar da sauran ‘yan jam’iyyar APC a kan hukuncin kotun.

Wamakko, ya ce ziyarar ‘yan-uwantaka ce, domin taya Yari da sauran shugabanni jaje.A na shi bangaren, Abdul-Aziz Yari ya ce hukuncin kotun kolin mukaddari ne daga Allah, wanda ba ya taba yin kuskure.

Leave a Reply