Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya karbi daliban
makarantar Kuriga da a ka kubutar su 137 a gidan gwamnatin
jihar.
Gwamnan ya bayyana cewar dalibai 137 da malami daya ‘yan bindigar su ka sace yayin da kuma rundunar sojin Nijeriya tayi nasarar kubutar da su gaba daya.
Tun a daren ranar Lahadi a ka kawo daliban jihar Kaduna sai dai sun kwana a hannun sojoji, inda a ka duba lafiyar su a asibitin sojoji na 44 kafin mika su hannun gwamnan jihar, a humkumance jiya Litinin.
A nashi bangaren Babban kwamandan runduna ta daya da ke Kaduna, Manjo Janar, Mayirenso Saraso, shi ne ya damka daliban ga gwamnan jihar, kuma ya yi bayanin yadda a ka kubutar da daliban.
Ya ce aikin hadin gwiwa ta hanyar hada karfin soji da kuma sasanci a ka yi amfani da su wajen kubutar da daliban wadanda su ka shafe kwanaki 16 a hannun ‘yan bindiga.