Home Labaru Labarun Ketare Ketare: Shirin Kawo Sojojin Haya Na Rasha Ya Tayar Da Hankali A...

Ketare: Shirin Kawo Sojojin Haya Na Rasha Ya Tayar Da Hankali A Afrika Ta Yamma

6
0
Masu zanga-zanga a Bamako, babban birnin Mali sun ɗaga tutar Rasha lokacin wata zanga-zangar nuna ƙin jinin Faransa a watan Mayu.

Masu zanga-zanga a Bamako, babban birnin Mali sun ɗaga tutar Rasha lokacin wata zanga-zangar nuna ƙin jinin Faransa a watan Mayu.

Akwai babbar fargaba a faɗin duniya game da tattaunawar da Mali ke yi da wani kamfani mai zaman kansa na sojojin Rasha mai suna Wagner group, amma ƴan Mali da dama na ganin sojojin Rashar ba za su iya maye gurbin dakarun Faransa ba a kwana-kwanan nan.

A shekarar 2013, an yi wa sojojin Faransa babbar tarba lokacin da suka isa Mali bayan da masu tada kayar baya suka ƙwace wasu yankuna kuma suka yi barazanar ƙwace iko gaba ɗaya ƙasar.

Amma kwanan nan Shugaba Emmanuel Macron ya ce zai janye rabin yawan dakarun Faransa masu ƙarfi su 5,000, kuma hakan ya zaburar da Firai Ministan Mali Choguel Maiga wanda ya zargi faransa da watsar da ƙasarsa.

Wannan ya haifar da zazzafan martani daga Faransa, inda Ministan Rundunar Sojojinta Florence Parly ta zargi gwamnatin Mali da “yin dumu-dumu da jinin sojojin Faransa.

Shugaba Macron ya ce ya yi matuƙar mamaki da zargin, kuma ya yi Allah wadai da gwamnatin Mali wadda ya ce ba ta da “ƴancin demokuraɗiyya” bayan juyin mulki biyu da aka yi cikin ƙasa da shekara guda.