Kungiyar malaman jami’o’i a Najeriya ta fara yajin aiki na makonni biyu.
Shugaban kungiyar na kasa Biodun Ogunyemi, ya sanar da fara yajin aikin bayan wani zaman da kwamitin zartarwar kungiyar ya yi a ranar litinin dinnan a Enugu.
Kungiyar ta ce ta yanke shawarar fara yajin aikin ne bayan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na dakatar da albashin malaman da ba su shiga tsarin albashin gwamnati na bai daya na IPPIS ba.
Haka
kuma, rahotanni sun nuna cewa kungiyar ta ASUU na fatan yajin aikin zai zaburar
da gwamnati ta sa hannu kan yarjejeniya daban-daban da kungiyar ta yi da
gwamnatin a shekarun 2009 da 2013 da 2017.
You must log in to post a comment.