Ma’aikatar wasanni a Najeriya ta bayyana shirinta na haramta duk wani wasan kwallon kafa na kwararru da babu ma’aikatan lafiya a filin wasa.
Ministan wasanni, Sunday Dare, ya bayyana haka yayin ganawar sa da manema labarai a ofishin sa a nan Abuja, bayan mutuwar wani dan wasan kungiyar kwallon kafa na Nasarawa United, Chineme Martins, ana tsaka da wasa a ranar Lahadi 8 ga watan Maris dinnan.
Dare, ya ce daga yanzu dole ne a tanadi kayayyakin kula da lafiyar ‘yan wasa, da jami’an lafiya a filin wasa kafin ma a fara wani wasa.
Ya ce ya tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar wasanni, kuma sun tsayar da cewa daga ranar 14 ga watan Maris wannan kudiri zai fara aiki.
Ministan
wasannin ya ce daga yanzu, an ba jami’an wasanni damar duba dukkanin kayayyakin
kula da lafiya a filin wasa, su kuma tabbatar suna aiki, da kuma tabbatar da
cewa jami’an lafiya na filin kafin su bari a fara wasa.
You must log in to post a comment.