Home Home Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa, Ari Ya Shiga Hannun ‘Yan Sanda

Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa, Ari Ya Shiga Hannun ‘Yan Sanda

32
0

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta sanar da kama Hudu dakataccen kwamishinan Hukumar Zabe ta jihar Adawawa Yunusa Ari, saboda yadda ya yi katsalandar a sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Muyiwa Adejobi ya fitar, ya ce Yunusa Ari ya na hannun ‘yan sanda.

Tun farko dai shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Baba Alkali, ya bada tabbacin kamawa tare da gudanar da binciken duk wadanda ke da hannun a batun siyasar Adamawa idan ya kama har da gurfanar da su a gaban kuliya.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 20 ga watan Afrilu ne shugaba Buhari ya amince a dakatar da jami’in har sai an kammala binciken da ‘yan sanda ke gudanarwa.

Leave a Reply