Home Home Gwamnati Ta Janye Tuhumar Rashawa Ta Naira Biliyan 1.84 Kan Mataimakin Dasuki

Gwamnati Ta Janye Tuhumar Rashawa Ta Naira Biliyan 1.84 Kan Mataimakin Dasuki

119
0

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami, ya janye tuhumar cin hanci da rashawa ta Naira biliyan 1 da miliyan 84 da ake yi wa tsohon mataimakin mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Nicholas Ashinz da wasu takwas.

Abubakar Malami dai ya janye karar ne a babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan ya karbi shari’ar a hannun hukumar yaki da da cikin hanci da rashawa EFCC, sai dai Lauyan da ya wakilci ministan a kotun David Kaswe bai bayyana dalilin janye karar ba.

A baya dai Hukumar EFCC ta kira shaidu bakwai a shari’ar, wadda aka fara tun shekaru biyar da su ka gabata.

Hukumar EFCC dai ta ta shirya dominn ci-gaba da sauraren karar, yayin da lauya daga ofishin ministan shari’a Mista Kaswe ya sanar da karbar karar daga hannun lauyan ta.

Lauyan EFCC Offem Uket, ya ce bai san cewa ofishin ministan shari’a ya karbi ragamar ci-gaba da sauraren karar ba, amma duk da haka bai yi musun janyewa ya maida karar zuwa ga lauya mai wakiltar ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ba.

Leave a Reply