Home Labaru Dakarun Sojin Najeriya Sun Hallaka Yan Bindiga 70 A Kaduna

Dakarun Sojin Najeriya Sun Hallaka Yan Bindiga 70 A Kaduna

828
0
Dakarun Sojin Najeriya Sun Hallaka Yan Bindiga 70 A Kaduna
Dakarun Sojin Najeriya Sun Hallaka Yan Bindiga 70 A Kaduna

Rundunar sojin kasa ta Nijeriya tare da hadin-gwiwar dakarun sojin sama sun kai hari kan ‘yan bindigar a dajin Kachia da ke jihar  Kaduna.

Mai Magana da yawun hedkwatan tsaron tarayya Manjo Janar John Enenche, ya bayyana haka a cikin  wata sanarwar da ya fitar, inda ya ce Sojin sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 70 a lokacin harin.

Ya ce, dakarun soji na rundunar Operation THUNDER STRIKE tare da hadin gwiwar rundunar Sojin sama ta bataliya ta 312 sun kai samame dajin Kachia, inda kuma su ka kashe wasu ‘yan bindiga da kuma barayin shanu.

Enenche ya kara da cewa, Sojojin sun kuma fatattake ‘yan bindigar daga garin Gidan Maikeri zuwa dajin da ke karamar hukumar Kachia.

Wannan dai ya biyo bayan rahoton da rundunar sojin ta samu cewa, an ga wucewar ‘yan bindigar cikin dajin, lamarin da ya sa rundunar sojin ta kai masu farmaki da jirgi mai saukar angulu, inda kuma su ka yi nasarar kashe kimanin ‘yan ta’adda 70.