Home Coronavirus Da Sauran Aiki A Yaki Da COVID-19

Da Sauran Aiki A Yaki Da COVID-19

483
0
Alkalumma: NCDC Ta Yi Wa Mutane 8, 003 Gwajin Cutar Covid-19
Alkalumma: NCDC Ta Yi Wa Mutane 8, 003 Gwajin Cutar Covid-19

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi karin haske bisa yadda cutar coronavirus ke cigaba da yaduwa a Nijeriya.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana haka a cikin a lokacin da ya ganawa da da kwamitin shugaban kasa a kan yaki da annobar COVID-19, wanda ya gudana a Abuja.

Boss Mustapha ya kara da cewa, har yanzu ba a kai ga kawo karshen annoba ba, kana ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su bi dokokin hukumomi domin takaita yaduwar COVID-19, tare da cewa gwamnati na bakin kokarin ta wajen yaki da annobar.

Sakataran ya ce ganin yadda masu dauke da cutar su ka karu a makon da ya gabata, kwamintin shugaban kasa da ke yaki da ya lura cewa, ba a ka kai ga kawo karshen annobar ba Nijeriya, matakin da ya ce dole a zage dantse wajen yin gwaji da killace masu dauke da cutar, tare da binciko wadanda ake zargin sun kamu, da kuma kula da wadanda cutar ta kama suka warke.

A karshe ya ce, karuwar yaduwar cutar a jihohi ya nuna a kwai bukatar al’ummar Nijeriya su natsu saboda kalubalen da ke tattare da lamarin, kuma lokaci ya yi da mutane za sub a gwamnati hadin kai wajen yaki da cutar.