Home Labaru Covid-19: Buhari Zai Bayyana Wasu Sabbin Matakai Nan Da Mako Mai Zuwa-NCDC

Covid-19: Buhari Zai Bayyana Wasu Sabbin Matakai Nan Da Mako Mai Zuwa-NCDC

545
0
Covid-19: Buhari Zai Bayyana Wasu Sabbin Matakai Nan Da Mako Mai Zuwa-NCDC
Covid-19: Buhari Zai Bayyana Wasu Sabbin Matakai Nan Da Mako Mai Zuwa-NCDC

Daraktan cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC Dakta Chikwe hekweazu, ya ce shugaban kasa Muhammadu zai bayyana wasu tsauraran hukunce-hukunce a kan yaki annobar Coronavirus.

Hekweazu ya tabbatar da cewa nan da ranar Laraba mai zuwa ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanar da gwamnoni tsauraran matakan.

Shugaban cibiyar ya bayyana haka ne a lokacin  da ya ziyarci gwamnan jihar Katsina Aminu Masari a gidan gwamnatin jihar da ke Katsina.

Chikwe hekweazu ya kuma bukaci gwamna Masari ya samar da wajen gwajin cutar COVID-19 a jihar Katsina, domin gaggauta samun sakamakon wadanda ake zargin su na dauke da cutar.

A nasa bangare, Masari ya ce ana tafiyar sa’o’i 12 daga jihar kafin a samu wajen gwajin cutar a Abuja, wanda a cewar sa samar da dakin gwajin a jihar zai taimaka wajen rage tsawon lokaci da wahalhanu kafin a samun sakamako gwajin.

RAHOTO: TARABA