Home Labaru An Ceto Mutum 24 Da Rushewar Gini Ya Rutsa Da Su A Abuja

An Ceto Mutum 24 Da Rushewar Gini Ya Rutsa Da Su A Abuja

37
0

Hukumomin bada agaji a Nijeriya sun ce, aƙalla mutane 24 aka ceto daga wani gini da ya rushe a birnin Abuja.

Haka kuma, Hukumoimin sun tabbatar da cewa akwai mutane uku da su ka rasu sakamakon munanan raunukan da su ka samu.

Ginin mai hawa uku dai, wanda aka yi shi da tsarin ginin ƙarƙashin ƙasa, ya rushe ne lokacin da ake ci-gaba da aikin gina shi a unguwar Gwarinpa.

Sai dai har yanzu babu tabbaci kan adadin mutanen da rushewar ginin ta rutsa da su, amma akasarin su leburori ne.