Home Labaru COVID-19: Za a janye sassaucin fita a Kaduna

COVID-19: Za a janye sassaucin fita a Kaduna

3294
0
Gwamnatin Kaduna ta ba jami'an tsaro umurnin daukar mataki kan masu karya dokar hana fita saboda coronavirus
Jihar Kaduna ta nuna bacin rai bisa yadda jama'a ke karya dokar hana fita.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba wa jami’an tsaro umurnin sanya kafar wando da masu karya dokar da ta sanya na hana fita a fadin jihar, domin hana yaduwar cutar coronavirus.

Gwamnatin jihar ta kuma yi barazanar dawo da dokar hana fita na awa 24 a jihar, da kuma soke sassaucin fita na kwana biyu da ta fara bayarwa a duk mako domin jama’a su samu damar tanadar abubuwan da za su bukata.

Mataimakiyar Gwamnan jihar, Hadiza Balarabe Sabuwa, ta nuna bacin rai bisa yadda jama’a ke karya dokar hana fitar da aka sanya domin dakile yaduwar cutar coronavirus a jihar Kaduna, duk da sassaucin da gwamnatin ta fara bayarwa na ranakun Talata da Laraba.

Ta kuma umurci jami’an tsaro cewa daga yanzu su rika sanya kafar wando da duk wanda suka samu yana karya dokar ta hana fita.

Hadiza Sabuwa ta ce masu sayar da kayan abinci da muhimman ababen bukata kadai aka amince wa fitar da kaya domin kasuwanci a ranakun Talata da Laraba a fadin jihar.

Ta kuma shawarci mutane da su takaita sayayyarsu zuwa kasuwannin da ke yankunansu, domin ba a amince da zuwa kasuwannin da ke nesa ba.

Sai dai ta yi karin haske cewa an yi sassauci ga manyan dillalen kayan abinci da muhimman ababen bukata, su yi lodi ko sauke lodi daga ranar Litinin har zuwa Juma’a.

Bayan haka mataimkiyar gwamnan ta ce bukaci jama’a da su lura da bayar da tazara a tsakaninsu a yayin da suka fita domin sayen kayan abinci da sauran muhimman bukatu.