Home Labaru Kiwon Lafiya Coronavirus ta kashe mutum 5,000 a rana guda

Coronavirus ta kashe mutum 5,000 a rana guda

652
0

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 a duniya ya zarce 68,000,  cikinsu har da mutane kusan dubu biyar da cutar ta kashe a kwana guda, yayin da ta harbi mutane sama da miliyan guda da dubu 200 a kasashe 191 na duniya.

Alkaluman Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya sun ce, a cikin sa’oi 24 kawai, mutane 4,690 suka mutu, yayin da aka samu sabbin mutane 75,522 da suka kamu da cutar a duniya.

Kasashen da aka fi samun mamatan cikin sa’o’i 24, sun hada da Amurka mai mutane sama da 1,000, sai Spain mai mutane 674 sannan Birtaniya mai mutane 621.

Har ila yau Italiya ke matsayin farko wajen yawan mutanen da suka mutu, inda suka kai 15,877 daga  cikin 128,948 da suka kamu, sai Spain wadda take da mutane 12,418 da suka mutu daga  cikin 130,759 da suka kamu, sannan Amurka wadda ta yi asarar rayukan mutane 9,180 daga cikin 324,052 da suka kamu.

Daga cikin mutane 68,125 da suka mutu a duniya, 49,137 sun fito ne daga nahiyar Turai, sai Asiya mai mutane 4,192, Gabas ta tsakiya na da 3,794, sannan Afirka da ke da mutane 431 daga cikin mutane 8,921 da suka kamu da cutar.