Home Coronavirus COVID-19: Za A Hana Shiga Jihohin Najeriya Na Sati 2

COVID-19: Za A Hana Shiga Jihohin Najeriya Na Sati 2

351
0
Gwamnonin sun kuma bukaci a samar da wadatattun kayan kariya ga ma'aikatan lafiya
Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta kuma bukaci a samar da wadatattun kayan kariya ga ma'aikatan lafiya

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 za su rufe iyakokin dukkan jihohin na tsawon kwana 14 domin dakile yaduwar annobar COVID-19.

Taron Kungiyar Gwamnonin Najeriya NGF ya yi ittifakin yin haka ne a makonni biyu masu zuwa.

Sun yanke shawarar ne bayan karbar rahoton yadda jihohin Lagos, Bauchi, Oyo da Ogun suke yaki da cutar da kuma irin darussan da suka koya daga annobar.

Gwamnonin sun kuma nemi a fadada yaki da cutar sabanin yadda a yanzu yake a karkashin kulawar gwamnatin tarayya.

Matakin da gwamnonin suka dauka ya biyo bayan samun fiye da mutum 117 da suka kamu da cutar ta COVID-19 a rana daya a kasar.

Shugaban kungiyar Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya ce dukkan gwamnonin sun amince su hana shiga jihohinsu daga wasu jihohi na tsawon mako biyu masu zuwa alokacin taron da suka yi ta bidiyo.