Home Labaru Maye Gurbi Kyari: Shugabanin APC Na Jihohi Sun Bada Shawara

Maye Gurbi Kyari: Shugabanin APC Na Jihohi Sun Bada Shawara

348
0
Maye Gurbi Kyari: Shugabanin Apc Na Jihohi Sun Bada Shawara
Maye Gurbi Kyari: Shugabanin Apc Na Jihohi Sun Bada Shawara

Kungiyar shugabanin jam’iyyar APC na jihohi ta bukaci shugabanin jam’iyyar na kasa su zabawa shugaba Muhammadu sabon shugaban ma’aikatan fadar sa.

Wata maiya ta ce, tuni an fara shirye-shiryen zaben wanda zai maye gurbin kujerar marigayi Abba Kyari ta shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Shawarar kungiyar na kunshe ne a cikin wata takardar ta’aziya bisa rasuwar Abba Kyari, wanda shugaban kungiyar kuma  shugaban jam’iyyar APC na jihar Borno Ali Bukar Dalori ya rattaba hannu.

A cewar sa, rasuwar Abba Kyari ta shafi shugabanin jam’iyyar duba da cewa, marigayin ne ke sada shugabanin jam’iyyar da shugaban kasa.

Dalori ya ce rasuwar Abba Kyari darasi ce ga ‘yan Nijeriya a kan batun zama a gida saboda coronavirus, duba da cewa cutar na iya kisa ko da mutum ya samu kulawar likitoci.

Ya kuma ja kunnen wadanda suke kokarin neman kujerar marigayi Abba Kyari su sani cewa, kujera ce wadda ke da muhimmanci wurin taimakawa shugaban kasa cimma manufofin sa.