Home Labaru Kiwon Lafiya Coronavirus Ta Ƙara Kama Mutum 2 A Kano

Coronavirus Ta Ƙara Kama Mutum 2 A Kano

366
0
Covid-19: Mutane 23 Sunsake Kamuwa A Jihar Kano, Jimilla 59
Covid-19: Mutane 23 Sunsake Kamuwa A Jihar Kano, Jimilla 59

An samu karin mutum 2 da suka kamu da cutar coronavirus kwana biyu bayan bullar cutar a jihar Kano. 

Mai Magana da yawun Gamna Abdullahi Ganduje, Salihu Tanko Yakassai ya ce yanzu jihar Kano na da mutum 3 da suka kamu da cutar.

Salihu Tanko Yakassai

Yakasai ya kara da cewa, an sake samun karin mutum 2 da suka kamu da cutar ne bayan fitowar sakamakon gwajin da aka yi musu, wanda ya tabbatar da cewa sun harbu da cutar.

A ranar Asabar ne aka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar Kano, bayan  mutumin ya yi tafiya daga Legas zuwa Abuja kafin isarsa zuwa jihar Kano.