Home Labaru Kiwon Lafiya Masu COVID-19 Sun Karu Zuwa 343 – NCDC

Masu COVID-19 Sun Karu Zuwa 343 – NCDC

228
0
Masu COVID-19 Sun Karu Zuwa 343 - NCDC
Masu COVID-19 Sun Karu Zuwa 343 - NCDC

Cibiyar takaita yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce an samu karin mutum 20 da suka kamu da cutar Coronavirus a Nijeriya.

Rahoton cibiyar na ranar  Litinin, 13 ga Afrilu ya ce, karin mutum 20 da su ka kamu da cutar,  sun hada da 13 a jihar Legas, 2 a jihohin Edo da Kano da kuma Ogun, sai guda a jihar Ondo.

NCDC ta ce yanzu Najeriya na da  mutum 343 da suka kamu da cutar.

Daga cikin adadin, mutum 91 sun warke, kana 10 sun mutu, yayin da ake ci gaba da jinyar mutum 242  a fadin kasar.