Home Labaru Kiwon Lafiya Coronavirus Ta Kama Kakakin Majalisar Jihar Edo

Coronavirus Ta Kama Kakakin Majalisar Jihar Edo

488
0
Coronavirus Ta Kama Kakakin Majalisar Jihar Edo
Coronavirus Ta Kama Kakakin Majalisar Jihar Edo

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Edo ya harbu da cutar coronavirus.

Yayin bayyana hakan, Mataimakin Gwamnan jihar, Philip Shuaibi, ya ce gwamnan jihar, Godwin Obaseki ya killace  kansa saboda zargin kamuwa da cutar.

Philip Shuaibi ya ce daukar matakin killace kai da gwamnan ya dauka ya biyo bayan cudanyar da ya yi ne da masu cutar.

Sanarwar ta ce gwamnan ya samu kusanci da Shugaba Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, da Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi, wadanda daga baya aka gano sun harbu da cutar.

Wakiliyarmu Nafisa Bello, ta ce akwai yiwuwar nan gaba shi ma Mataimakin Gwamnan da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar da suka yi hulda da Gwamna Obaseki, bayan ganawarsa da Abba Kyari da Bala Muhammad, su ma za su killace kansu.

Philip Shuaibi ya kara da cewa kamuwar Kakaki Majalisar Dokokin jihar Frank Okiye, da coronavirus ta tabbata ne bayan gwajin da aka yi masa bayan dawowarsa daga kasar Birtaniya.

 Tuni dai Okiye ya fara nuna alamun rashin lafiya, tun bayan dawowarsa daga Birtaniya a karshen makon da ya gabata.

Wasu majiyoyi sun ambato cewa an ga Okiye sanye da abun rufe fuska bayan saukarsa a Abuja, kafin ya wuce zuwa Benin.

Wasu masu sharhi na ganin kamata ya yi tun da farko Okiye ya killace kansa bayan dawowarsa daga Birtaniya.