Home Labaru Kiwon Lafiya Ana Gina Ɗakunan Gwajin Coronavirus 5 A Arewa

Ana Gina Ɗakunan Gwajin Coronavirus 5 A Arewa

459
1
Kawo yanzu mutum 50,000 sun kamu da cutar coronavirus a kasar Iran.
Gwamnatin Iran na shan mummunan suka kan matakanta na yaki da annobar cutar coronavirus.

Gwamnatin tarayya na gina sabbin dakunan gwajin cutar coronavirus guda biyar a Arewacin Najeriya.

Ana gina sabbin dakunan gwamin cutar ne a jihohin Kano, Kaduna, Filato, Sokoto, Borno, Rivers da Ebonyi.

Karon farko ke nan da za a samar da dakunan gwajin coronavirus a Arewacin Najeriya, mai jiha 19, masu dauke da fiye da rabin al’ummar kasar.

Ginin sabbin cibiyoyin na daga cikin matakan da Najeriya ke duka na yaki da annobar cutar, da ke kara yaduwar a sassan kasar.

Cibiyar Hana Yaduwar Cuttuka ta Kasa (NCDC) ta ce hakan zai kara yawan cibiyoyin daga 6 da ake da su zuwa 13.

Shugaban NCDC Dr. Chike Ihekwazu ya ce, “Aiki ya yi nisa a biranen Abakaliki, Maiduguri, Kano, Kaduna, Sokoto, Jos, da Fatakwal.

A baya an ‘yan kasar sun yi ta nuna damuwa game da karancin dakunan gwajin cutar a kasar, musamman a yankin Arewa wanda shi ne mafi fadin kasa da yawa al’umma.

A halin yanzu kasar mai yawan al’umma kusan miliyan 200 da jiha 36, na na da dakunan gwajin coronavirus guda shida.

4 daga cikin cibiyoyin shidan na yankin Kudu maso gabashin kasar, sai 1 a jihar Edo, 1 a Babban Birnin Tarayya Abuja. Daga cikinsu 2 na jihar Legas, 1 a Abuja, 1 a Edo, 1 a Ogun, 1 a Osun.

Amma a wata sanarwa da hadimin shugaban kasar kan shafukan zumunta Bshir Ahmad ya fitar, ya ce aiki ya yi nisa a kokarin gina karin cibiyoyin gwajin cutar.