Home Labaru Kimiyya Cutar Coronavirus: ‘Hassada Ce Ta Sa Ake Alakanta 5G

Cutar Coronavirus: ‘Hassada Ce Ta Sa Ake Alakanta 5G

331
0

Ana ci gaba da tafka muhawara a kasashen duniya game da alaka tsakanin annobar coronavirus da manhajar sadarwar ta 5G, inda wasu ke da yakinin cewa, sabuwar fasahar ta 5G, ita ce silar barkewar coronavirus wadda ta lakume rayuka kusan dubu 70 a sassan duniya.

Sai dai wasu masana harkar sadarwar sun ce, ko kadan babu abin da ya danganta cutar da 5G.

Wani masanin fasahar sadarwa a Najeriya Umar Saleh Gwani, ya ce, babu alaka tsakanin wannan annoba da hanyar sadarwar 5G, hasali ma, hassadar da ake yi wa China ce, ta sa wasu ke alakanta cutar da 5G.

Gwani ya bayyana cewa, a baya-bayan nan, kasar China ta yi wa takwarorinta irin su Amurka da kasashen Turai fintinkau a bangarorin  kimiya da fasaha da kere-keren makamai na zamani har ma da harkar kasuwanci, abinda ya sa ake yi wa Chinan zagon kasa bayan ta kaddamar da gagarumar fasahar 5G tare da hadin guiwar kamfanin Huawei.

A cewar masanin, fintinkau din da China ta yi wa manyan kasashen duniya, ya girgiza ginshikin tsarin jari hujja a duniya, lamarin da ya yi sanadiyar karyewar hada-hadar kasuwanci a hannayen jari na Wall-Street dake birnin New York na Amurka.