Gwamantin kasar Italiya ta dauki matakin killace ‘yan kasar baki daya har zuwa ranar uku ga watan gobe a wani mataki na dakile yaduwar cutar Covid-19 da ke ci gaba da kamari.
Shugaban kasar Giuseppe Conte, ya tabbatar da dokar tabacin wacce ake sa ran za ta takaita shige da ficen ‘yan kasar kimanin miliyan 60 a wani yunkuri na kawar da cutar daga kasar wacce ita ce kan gaba wajen samun bullar cutar a nahiyar turai.
Dokar
ta kuma bayyana matakin soke duk wasu tarukan jama’a, da dukkan wasannin motsa
jiki, tare da mayar da wuraren wasannin a matsayin asibitocin wucin gadi ga
masu wasannin motsa jikin da aka samu sun kamu da cutar.