Home Labaru Siyasar Guinea-Bissau: ECOWAS Ta Fusata

Siyasar Guinea-Bissau: ECOWAS Ta Fusata

248
0
Siyasar Guinea-Bissau: ECOWAS Ta Fusata
Siyasar Guinea-Bissau: ECOWAS Ta Fusata

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta ce ta soke yunkurin ta na shiga tsakani a rikicin shugabancin kasar Guinea-Bissau.

Tun da farko dai ECOWAS ta so ganawa da bangarorin dake rigima da juna a wannan makon, sai dai a sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce ta sauya matsayar ta bayan bangaren Shugaba Umaro Sissoco Embalo, ya zarge ta da yin azarbabi wajen shiga maganar.

Guinea-Bissau dai ta kasance cikin rikita-rikitar siyasa tun cikin watan Disambar bara, lokacin da hukumar zaben kasar ta bayyana dan takara na jam’iyyar adawa Umaro Sissoco Embalo, a matsayin wanda ya doke Domingos Simoes Pereira, dan takarar jam’iyya mai mulki ta PAIGC.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta bukaci a yi amfani da sulhu da tattaunawa wajen warware wannan rikici.