Home Labaru Kiwon Lafiya Nijeriya Zata Hana Shigowar Jiragen Sama Daga Kasashen Waje

Nijeriya Zata Hana Shigowar Jiragen Sama Daga Kasashen Waje

245
0

A ci gaban da yunkurin dakile yaduwar annobar Coronavirus, Najeriya za ta hana shigowar jiragen sama daga kasashen waje.

Mai taimaka wa shugaban Najeriya kan kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad, ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Bashir Ahmad ya ce sabon matakin na Gwamna Tarayya zai fara aiki ne daga ranar Litinin 23 ga watan Maris da muke ciki.

Ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da karin bayani game da matakin.