Home Labaru Kiwon Lafiya Ciwon Sikila: Yin Gwajin Jini Kafin A Yi Aure Shi Ne Mafita...

Ciwon Sikila: Yin Gwajin Jini Kafin A Yi Aure Shi Ne Mafita Ga Ma’aurata – Likitoci

622
0

Ranar 19 ga watan Yuni na kowace shekara ce, kungiyoyin duniya su ka kebe domin wayar da kan mutane game da ciwon Sikila.

Malaman kiwon lafiya dai sun ce ana gadon cutar, lamarin da ya sa su k ace ya zama wajibi idan mutane za su yi aure su tabbatar sun yi gwaji.

Alamomin cutar kuwa sun hada da kumburin kafa da hannu, da ciwon ido da kamuwa da cututtuka irin su hawan jini da shanyewar bangaren jiki da sauran su.

Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta gudanar ya nuna cewa, akan haifi sama da yara 300,000 a duniya dauke da wannan ciwo, kuma kashi 75 cikin 100 daga cikin su daga kudancin Saharar Afrika su ke, yayin da kashi 66 cikin 100 daga Nijeriya ake samun su.

Rashin yin gwajin jinni da rashin sani musamman a yankunan karkara, ya na daga cikin matsalolin da ke sa cutar na ci-gaba da yaduwa musamman a Nijeriya.

Leave a Reply