Wani jigon jam’iyyar APC kuma shugaban kwanitin ladabtarwa na jam’iyyar reshen jihar Kano Alhaji Haruna Zago, ya ce a wani mataki na ba mata da yara dama a gwamnatin APC, akwai bukatar A’isha Buhari ta mallaki ofishin ‘First Lady’ domin ci-gaban kasar nan.
Ya ce jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta goyi bayan A’isha Buhari a matsayin ‘First Lady’, duba da ayyukan agaji da ta ke yi ba tare da ofishin ‘First Lady’.
Haruna Zago ya kara da cewa, idan ofishin ‘First Lady’ ya fara aiki, za a cimma nasarori da dama musamman a bangaren mata da matasa.
A cewar sa, ba laifi ba ne a bar ofishin ‘First Lady’ ya yi aiki, kamar yadda yin hakan ba zai saba wa kundin tsarin mulki ba, kuma za a cimma manufofi masu amfani ta hakan.