Home Labaru Zargin Zagon-Kasa: Abdul-Aziz Yari Ya Kalubalanci Rahoton Kwamitin APC

Zargin Zagon-Kasa: Abdul-Aziz Yari Ya Kalubalanci Rahoton Kwamitin APC

429
0

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya bayyana rahoton da kwamitin mutane biyar na jam’iyyar APC su ka gabatar, wanda ke zargin sa da yi wa jam’iyyar zagon kasa a matsayin raini da kuma tozarci a gare shi.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan Ibrahim Dosara, ya ce ikirarin kwamitin da kuma abubuwan da ake wallafawa a kafofin yada labarai ba su da fa’ida, sun kuma saba ma hukunci da umurnin kotu.

Abdul-Aziz Yari, ya ce rahoton kwamitin ya haddasa tarin tozarci da batanci gare shi.

Rahoton kwamitin dai ya zargin cewa, rawar da Abdul-Aziz Yari da Lawal Shu’aibu su ka taka a zaben shekara ta 2019 ya taimaka wajen rashin nasarar jam’iyyar a jihar Zamfara.