Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa, ta ce ta na duba yiwuwar ware Naira biliyan 702 a matsayin tallafi ga ma’aikatan gwamnati, a wani ɓangare na matakan daƙile raɗaɗin cire tallafin man fetur da aka yi.
Yayin zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya ce shiga tsakani ya haɗa da ƙudirin da aka bada shawarar daga Naira biliyan 23 da rabi zuwa Naira biliyan 45 duk wata a matsayin alawus-alawus na man fetur ga ma’aikatan gwamnati.
Ya ce Majalisar ta samu shawarwari a kan hanyoyi daban-daban da kuma yadda Nijeriya za ta iya amfani da duk wani kari da ake samu cikin kuɗaɗen shiga domin rage tasirin da hakan zai haifar ga rayuwar ma’aikata.
Gwamna Bala Mohammed ya sun bada shawarar a yi gyara, inda aka ƙiyasta kudin da ya kai Naira biliyan 702 da miliyan 92 a matsayin wani ɓangare na alawus-alawus da ya kamata a ware a matsayin na cire tallafin man fetur ga duk ma’aikata da kuma bada Naira biliyan 23 ko 25 duk wata domin dakile raɗaɗin cire tallafin.