Home Labaru Hankula Sun Tashi Yayin Da EFCC Ta Gayyaci Tsofaffin Ministocin Buhari 8

Hankula Sun Tashi Yayin Da EFCC Ta Gayyaci Tsofaffin Ministocin Buhari 8

287
0

Rahotanni na nuni da cewa, Hukumar EFCC ta na binciken
wasu daga cikin tsofaffin ministoci takwas da su ka yi aiki a
karkashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari .

Rahotanni sun ce, an gayyaci ministocin ne bisa zargin aikata laifuffukan cin hanci da rashawa.

Katunan gayyatar sun buƙaci tsofaffin ministocin su yi bayanin yadda su ka kashe kuɗaɗen da aka ware wa ma’aikatun su domin gudanar da ayyuka a lokacin da su ke riƙe da muƙaman gwamnati.

Wani babban jami’in hukumar EFCC da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce baya ga tsohuwar ministar harkokin mata Pauline Tallen da aka gayyata a makon da ya gabata bisa zargin almundahanar Naira biliyan 2, an kuma gayyaci ƙarin wasu ministoci bakwai.

Leave a Reply