Jagora a yankin Neja Delta Asari Dokubo, ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu cewa kada ya saki shugaban haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu.
Dokubo Asari ya bayyana haka ne, yayin tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda ya ce ya ce sakin Nnamdi Kanu tamkar farfado ayyukan kashe mutane da ta’addanci ne, kuma hakan zai zama tamkar tukwici ne ga laifuffukan da ya aikata, don ya ce ya kamata Nnamdi kanu ya fuskanci shari’a.
Idan dai za a tunawa, tun lokacin da aka sake kama Nnamdi Kanu a shekara ta 2021 ya ke tsare a hannun hukumar DSS, inda ya ke fuskantar shari’ar zargin ta’addanci.
A shekara ta 2017 ne, kotun tarayya da ke Abuja ta bada belin Nnamdi Kanu, amma ya karya ka’idojin belin sa, lamarin da ya sa ya gudu zuwa kasar waje, amma sannu a hankali jami’an tsaro su ka sake kamo shi.














































