An ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele a babbar kotun tarayya da ke nan Abuja, inda aka tabbatar wa kotu cewa binciken kimiyya ya nuna cewa an yi amfani da sa hannun bogi na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wajen cire kuɗi dala miliyan 6.2 domin daukar nauyin masu sanya idanu na ƙetare a zaɓe.
Wani shaida da EFCC ta kira, Bamaiyi Meriga ya tabbatar wa kotu ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Hamza Muazu cewa binciken kimiyya da aka yi wa takardun da aka sanya hannu a kan su don cire kudin ya nuna cewa sa hannu da hatimi da aka yi amfani da su wajen cire kudin ba daidai suke da na ainihi ba.
Ya kuma tabbatar da cewa sa hannun ba na tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba ne, kuma ba na tsohon sakataren gamnatin tarayya, Boss Mustapha ba ne.
An gabatar wa alƙalin da ke jagorantar shari’ar takardun biyu, masu ɗauke da umarnin shugaban ƙasa a matsayin shaida, sannan kuma ya amince da su.
Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa, ya nuna rashin amincewar sa da shaidar, yana mai cewa shaidar ya yaudari kotun ne don kauce wa tambayoyin da za a yi masa, sai dai lauyan masu shigar da ƙara, Rotimi Oyedepo, bai ji dadin kalaman lauyan wanda ake ƙarar ba.
An dai ɗage shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Maris domin ci gaba da shari’ar.