Ministan Lantarki, Bayo Adelabu, ya yi barazanar kwace lasisin kamfanonin rarraba wuta na Discos, yana mai cewa ba za a lamunci yanayin da suke saka mutane cikin duhu ba.
Ministan, wanda ya wallafa sakon barazanar a shafin sa na X a ranar Laraba Ya ce ya damu matuka da tabarbarewar samar da wuta da ake fama da rashin ta a fadin kasa.
Ya ce ya kira taron ne don tattaunawa kan yadda ake matukar fama da matsalar samun wuta a wadannan yankunan da kuma nemo mafita.
Ya ce yanzu haka dai ana matukar fama da karancin wuta a wasu sassan Nijeriya, musamman babban birnin tarayya, Abuja a daidai lokacin da yanayin zafi ke kara kunno kai.
Sai dai Mista Adelabu ya bayyana cewa duk da wannan ci gaba da ake samu, wasu kamfanonin sun gaza rarraba wutar da TCN ke bayarwa yadda ya kamata.
Ya kuma koka kan yadda yawan barnar kayayyakin samar da wutar da ake yi ke kara ta’azzara matsalar a Abuja da Benin da Fatakwal da kuma Ibadan.
Minista Adelabu ya sha alwashin cewa daga yanzu zai kama dukkan kamfanonin rarraba wutar da alhaki idan har ba su yi abin da ya dace ba.