Home Labaru Rattaba Hannu: Shugaba Tinubu Zai Sake Fasalin Fannin Mai Da Iskar Gas

Rattaba Hannu: Shugaba Tinubu Zai Sake Fasalin Fannin Mai Da Iskar Gas

41
0

Shugaban kasa BolaAhmad Tinubu ya rattaba hannu kan dokar sake fasalin man fetur da iskar gas domin ya sanya Najeriya a matsayin kasar da aka fi son zuba jari a bangaren mai da iskar gas a Afirka.

A cewar wata sanarwa da mai ba Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce an tsara da kuma sauya manufofin ne tare da hadin gwiwar manyan ma’aikatu da hukumomi kamar ma’aikatar shari’a ta tarayya, da ma’aikatar kudi ta tarayya, da ma’aikatar man fetur ta tarayya, da ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta tattalin arziki ta tarayya, da ma’aikatar tattara kudaden shiga ta kasa, da kuma hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa ta Najeriya.

Ya ce an yi gyare-gyaren ne domin kara habaka tattalin arzikin Najeriya da kuma kara karfin ta a kasuwar mai da iskar gas ta duniya.

Ya ce ma’aikatar yada labarai ta tarayya da wayar da kan jama’a ta kasa za ta sanar da cikakkun bayanan a hukumance, wanda zai nuna wani gagarumin mataki na samun ci gaba mai inganci a bangaren mai da iskar gas a Najeriya.

Ya ce mai ba Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin makamashi zai ya ci gaba da hada kai da duk masu ruwa da tsaki da aka ambata kan yadda ake aiwatar da wadannan umarni, tare da jaddada kudirin gwamnatin na samar da ci gaba mai dorewa da ci gaba a masana’antar makamashi

Leave a Reply