Home Labaru Hare-Haren Syria: Erdogan Na Shirin Ziyartar Rasha

Hare-Haren Syria: Erdogan Na Shirin Ziyartar Rasha

228
0

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan zai ziyarci birnin Moscow na Rasha a mako mai kamawa, ziyarar da ke zuwa bayan wasu hare-hare ta sama kan jerin gwanon motocin Sojin Turkiyan a Syria.

Ziyarar bazatan wadda Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya sanar da kan sa tun a ranar juma’a, ana ganin za ta mayar da hankali kan yadda dakarun Bashar al-Assad, ke gab da kwace ikon yankin Idlib marikar ‘yan tawaye ta karshe a arewa maso yammacin Syrian.

Mai Magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov

Mai Magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov, wanda ya sanar da ziyarar ta Erdogan, da zata gudana a ranar 27 ga wannan watan bai bayyana hakikanin makasudin ziyarar da kuma batutuwan da za a tattauna ba.

A bara dai Turkiyya mai marawa ‘yan tawaye baya, da kuma Rasha babbar mai goyon bayan gwamnatin kasar, sun cimma yarjejeniyar ganin an kare fararen hula a yankin na Idlib.