Home Labaru Cin Zarafi: Jami’an Tsaro Sun Kama Malamin Firamare Da Yi Wa Dalibar...

Cin Zarafi: Jami’an Tsaro Sun Kama Malamin Firamare Da Yi Wa Dalibar Sa Fyade A Adamawa

420
0
Abdullahi Nurudeen, Shugaban Hukumar Civil Defence Jihar Adamawa
Abdullahi Nurudeen, Shugaban Hukumar Civil Defence Jihar Adamawa

Shugaban hukumar Civil Defence na jihar Adamawa Abdullahi Nurudeen ya ce, jami’an su sun samu nasarar kama wani malamin makarantar firamare a karamar hukumar yola ta kudu mai suna  Nathan Yusuf mai shekaru 37 bisa zargin sa da yiwa dalibar shi mai shekaru 14 fyade.

Malamin ya amince da aikata laifin, dai ya ce ya bata maganin bacci ne kafin ya samu damar yin lalata da ita.

Shugaban hukumar Civil Defence Abdullahi Nurudeen ya ce da zarar sun kammala gudanar da bincike a kan lamarin, zamu mika mai laifin zuwa kotu,  sannan kuma ya shawarci  iyayen daliban  su rika sa ido a kan ‘ya’yan su, sannan su kai rahoton duk wani al’amari da ba su gane taketaken sa ba.