Home Labaru Tsaro: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Amince Da Jami’an ‘Yan Sintiri A Fadin...

Tsaro: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Amince Da Jami’an ‘Yan Sintiri A Fadin Nijeriya

229
0
’Yan Sanda
’Yan Sanda

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya na ci gaba da horar da ‘ya’yan kungiyar ‘yan sintiri a kwalejojin horar da ‘yan sanda daban daban da ke fadin Nijeriya.

Kwamandan kungiyar Ali Sokoto, ya bayyana haka a lokacin da ya ke mikwa manema labarai takardun izini da kungiyar ta samu daga ‘yan sandan Nijeriya.

Ya ce aikin na hadin gwiwa ne, a tsakanin rundunar ‘yan sandan Nijeriya da wani kamfanin wanda aka amince masa wajen horar da jami’an tsaro daban daban.

Ali Sokoto ya kara da cewa,  saboda haka ya na kira ga ‘ya’yan kungiyar musamman wadanda ke samun horon su dage wajen koyon dukkannin abinda  rundunar za ta koyar da su.

Ya tabbatar da cewa, a wannan karon an raba aikin horon ne zuwa shiyya-shiyya, da suka hada da  kudu maso kudu, da arewa ta tsakiya da arewa maso yamma da arewa da kudu maso arewa da arewa maso gabas.

A yanzun rundunar ta kammala ba ‘yan kungiyar horo a jihohin Nasarawa da Niger da kuma Abuja, inda za a ci gaba da na jihohin shiyyar kudu maso yammacin Nijeriya nan bada jimawa ba.