Shugaban hukumar Civil Defence na jihar Adamawa Abdullahi Nurudeen ya ce, jami’an su sun samu nasarar kama wani malamin makarantar firamare a karamar hukumar yola ta kudu mai suna Nathan Yusuf mai shekaru 37 bisa zargin sa da yiwa dalibar shi mai shekaru 14 fyade.
Malamin ya amince da aikata laifin, dai ya ce ya bata maganin bacci ne kafin ya samu damar yin lalata da ita.
Shugaban
hukumar Civil Defence Abdullahi Nurudeen ya ce da zarar sun kammala gudanar da
bincike a kan lamarin, zamu mika mai laifin zuwa kotu, sannan kuma ya shawarci iyayen daliban su rika sa ido a kan ‘ya’yan su, sannan su kai
rahoton duk wani al’amari da ba su gane taketaken sa ba.

