Home Labaru Cike Gurbi: An Rantsar Da Sabon Ɗan Majalisar Jam’Iyyar PDP A Kaduna

Cike Gurbi: An Rantsar Da Sabon Ɗan Majalisar Jam’Iyyar PDP A Kaduna

13
0

Kakakin majalisar dokoki ta jihar Kaduna Yusuf Zailani, ya rantsar da sabon ɗan majalisa Usman Ali-Baba na jam’iyyar PDP.

Ali Baba dai shi ne sabon ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Sabon Gari a majalisar dokoki ta jihar Kaduna.

Idan dai ba a manta ba, Ali Baba  ya lashe zaɓen maye gurbin da ya ya gudana ranar 20 ga watan Yuni na shekara ta 2021 a mazaɓar Sabon Gari.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan rantsar da shi, Ali Baba ya gode wa da kakakin majalisa da sauran ‘yan majalisa da kuma jam’iyyar PDP, sannan ya gode wa al’ummar mazaɓar Sabon Gari bisa ganin cancantar sa har su ka amince ya wakilce su a majalisar dokoki ta jihar.