Home Labaru Cin Bashi: Sanata Ndume Ya Koka Da Yawan Tulin Bashin Da Buhari...

Cin Bashi: Sanata Ndume Ya Koka Da Yawan Tulin Bashin Da Buhari Ke Ciwowa

18
0
Sanata Ali Muhammad Ndume

Dan majalisar dattawa Sanata Ali Ndume, ya nuna matuƙar damuwa ganin yadda Shugaba Buhari ke shirin kinkimo wa Nijeriya karin bashi.

Sanatan, ya kuma nuna damuwa ganin yadda Majalisar Dattawa ta ke rawar-jikin amincewa da dukkan buƙatu da dalilan ciwo bashin da Buhari ke gabatar mata.

Ya ce abin haushi da takaici, har yanzu babu wasu muhimman ayyukan raya ƙasa da za a iya tinƙaho da su, waɗanda za a ce an gina su ne daga cikin maƙudan kuɗaɗen bashin da ake ciwowa.

Sanatan ya bayyana haka ne a wata zantawa da ya yi da manema labarai a Abuja, yayin da ya ke tsokaci game da bashin da shugaba Buhari ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin ya ciwo, waɗanda kuɗaɗen a yanzu za su iya kai naira tiriliyan 2 da biliyan 200.