Home Labaru Batun Rusa Masallaci: Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa Ta Ce Kanzon Kurege...

Batun Rusa Masallaci: Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa Ta Ce Kanzon Kurege Ne

742
0

Gamayyar kungiyoyin matasan Arewa, wato Coalition of Northern Youth Groups, a turance ta karyata zargin da a ke yayatawa cewa gwamnan Jihar Rivers, Nysom Wike, ya bayar da umurnin rusa wani Masallaci a Fatakwal.

Kungiyar ta ce hakan bai faru ba, karya ce da ‘yan siyasa ke yadawa domin haifar da rikicin kabilanci da na addini ko na bangaranci domin biyan bukatun kan su.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta rabawa manema labarai a Kaduna, shugaban da ya hada taron kungiyoyin Mohammed Sani, ya ce daga bayanan da su ke da su, gwamnan Jihar Rivers yana kula da hakkokin mabambanta Addinai fiye da wasu gwamnonin da suke zarginsa da kin jinin Addinin na Musulunci.

 Ya ce gwamna Nysom Wike, na da kyakykyawar dangantaka da arewa da kuma ‘yan arewa, kuma tamkar dan’uwa yake ga al’ummar Musulmai.

Ya ce a lokacin da suka sami labarin cewa an rusa wani Masallaci a Fatakwal, kungiyar su ta gudanar da bincike na musamman inda ta gano cewa ginin da ake cewa Masallaci wani gini ne na wani mutum wanda kuma ba shi da takardun izinin fara wannan ginin.