Home Labaru Cigaban Kasashen Afirka: Shugaba Buhari Zai Bar Najeriya Zuwa Kasar Japan

Cigaban Kasashen Afirka: Shugaba Buhari Zai Bar Najeriya Zuwa Kasar Japan

925
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar birnin Abuja zuwa kasar Japan domin halartar taron cigaban kasashen Afrika na bakwai.

Sanarwar hakan ta fito ta bakin mai taimaka masa na musamman akan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Femi Adesina

Femi Adesina

Ya ce wannan shine karo na biyu da shugaba Buhari zai halarci wannan taron, bayan wanda ya halarta a birnin Nairobi na kasar Kenya a shekarar 2016.

An shirya taron ne na kasashen duniya a Tokyo, domin samun hanyoyin da za a kawo ci gaba ga yankin Afirka, wanda za ayi a birnin Yokohama ranar 28 ga wannan watan sannan a gama ranar 30 ga wata.

Ana sa ran Shugaban kasar zai yi magana akan Najeriya a wajen sannan kuma zai yi magana akan dangantakar dake tsakanin Najeriya da Japan.

Bayan an kammala taron shugaban zai halarci wata walima, sannan kuma zai amsa gayyatar da Sarki Naruhito yayi masa zuwa fadarsa dake Tokyo.